Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
 
• Firaministan kasar Sin ya tashi zuwa kasar Masar don halartar taron ministoci tsakanin Sin da Afrika 2009-11-06
A ran 6 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya tashi zuwa kasar Masar don yin ziyara, kuma zai halarci bikin bude taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a kwana biyu masu zuwa a birnin Sharm El Sheikh. Firaministan kasar Sin ya kai ziyara a Afrika don ingiza hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika da kasar Masar da kuma kasashen Larabawa.
• Jama'a 'yan kabilu daban daban na kasar Sin suna murnar cika shekaru 60 da kafuwar kasarsu 2009-10-07
Ran 1 ga wata rana ce ta cika shekaru 60 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, a sabili da haka, jama'a 'yan kabilu daban daban na kasar Sin sun gudanar da bukukuwa iri daban daban, domin yin murnar wannan ranar. Jihar Guangxi mai cin gashin kanta ta kabilar Zhuang da ke kudancin kasar Sin jiha ce da ta fi yawan 'yan kananan kabilu a kasar Sin. Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, an sami manyan sauye-sauye a jihar Guangxi.
• Hu Jintao ya yi muhimmin jawabi a yayin babbar muhawara ta babban taron M.D.D. a karo na 64 2009-09-24
Ran 23 ga wata, a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, an kaddamar da babbar muhawara ta babban taron Majalisar Dinkin Duniya a karo na 64, inda kuma a cikin makon da muke ciki, shugabanni fiye da 140 na kasashen duniya suka yi shirin ba da jawabai kan inganta gudanar da harkoki a tsakanin mabambantan bangarori da yin tattaunawa a tsakanin al'adu daban daban da nufin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasuwa a duniya.
• Tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikaya aiki ne iri daya na kasashen Sin da Amurka 2009-09-09
Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an gudanar da dandlin tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikaya tsakanin kasashen Sin da Amurka a ranar 8 ga watan da muke ciki a birnin Phoenix yayin da shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Wu Bangguo ke yin ziyara a kasar Amurka.
• Rangadin gani da ido a shahararren kauye mai samar da makamashi irin na halittu a Jamus 2009-08-27
Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, kauyen Juhnde na birnin Gottingen na jihar Niedersachsen ta kasar Jamus, wani kyakkyawan kauye ne dake da mutane sama da 700 kawai, amma ya yi suna sosai a kasar Jamus saboda shi ne kauye na farko mai samar da makamashi irin na halittu a kasar ta Jamus da ma Nahiyar Turai.
• Hillary Clinton ta mai da hankali kan yanayin tsaro a muhimmin yankin fitar da man fetur dake Nijeriya 2009-08-13
A ran 12 ga wata, yayin da take yin shawarwari da jami'an Nijeriya, sakatariyar harkokin waje ta Amurka Hillary Clinton, wadda ke ziyara a nahiyar Afirka, ta mai da hankali sosai kan yanayin tsaro da ake ciki a muhimmin yankin fitar da man fetur na Nijeriya, wato yankin Neja Delta.
• Inganta huldodin kasashen Sin da Amurka ta fuskar cimma moriyar juna a karni na 21 2009-07-30
Kwanan baya, an kammala shawarwarin kasashen Sin da Amurka a zagaye na farko kan manyan tsare-tsare da harkokin tattalin arziki a Wangshinton D.C., hedkwatar kasar Amurka. A yayin taron yini biyu, jami'an kasashen biyu sun yi tattaunawar keke da keke kan muhimman batutuwan dake shafar bangarorin biyu, da shiyya-shiyya, gami da kasa da kasa.
• Kungiyar kasashen 'yan-ba-ruwanmu tana zura ido wajen yin gyare-gyare da kanta da moriyar kasashe masu tasowa 2009-07-16
Ran 15 ga wata a birnin Sharm El Sheikh da ke bakin kogin Maliya na kasar Masar, an bude taron koli na kungiyar kasashen 'yan-ba-ruwanmu a karo na 15 wanda za a shafe kwanaki biyu ana yinsa. Masu bincike sun yi nuni da cewa, yadda kungiyar za ta sami sabon karfi, yadda za a iya kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da kuma yadda za a iya tinkarar manyan harkokin duniya za su zama muhimman batutuwan da za a tattaunawa cikin wannan taron koli.
• Jam'iyyar kwaminis ta Sin na kara mai da hankali a kan sauraron ra'ayoyin jama'a domin inganta kanta a sabon halin da ake ciki 2009-07-01
Laraba 1 ga watan Yuli rana ce ta cika shekaru 88 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta Sin, wato jam'iyyar da ke jan ragamar mulkin kasar Sin. To, a cikin shekarun nan 88 da suka wuce, har kullum jam'iyyar na son sauraron ra'ayoyin jama'a domin inganta kanta.
• Ganawa ta farko a tsakanin shugabannin kasashen BRIC 2009-06-17
A ran 16 ga wata a birnin Yekaterinburg na kasar Rasha, an gudanar da shawarwari a karo na farko a tsakanin shugabannin kasashe hudu da ake kira BRIC, wato Brazil da Rasha da Indiya da kuma Sin, wadanda tattalin arzikinsu ke bunkasa cikin sauri. A lokacin da ake fama da matsalar kudi a duniya.
1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19