|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-07-01 18:23:16
|
Jam'iyyar kwaminis ta Sin na kara mai da hankali a kan sauraron ra'ayoyin jama'a domin inganta kanta a sabon halin da ake ciki
cri
Laraba 1 ga watan Yuli rana ce ta cika shekaru 88 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta Sin, wato jam'iyyar da ke jan ragamar mulkin kasar Sin. To, a cikin shekarun nan 88 da suka wuce, har kullum jam'iyyar na son sauraron ra'ayoyin jama'a domin inganta kanta. A gun taron ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da aka kira a kwanan baya, an gabatar da daga matsayin gamsuwar jama'a a wajen binciken ayyukan shugabannin jam'iyyar. Sa'an nan kuma, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar, Mr.Hu Jintao ya jaddada cewa, a sabon halin da ake ciki, dole ne a dora muhimmanci a kan raya dimokuradiyya a cikin jam'iyyar, ta yadda za a gudanar da harkokin mulki bisa kimiyya da dimokuradiyya da kuma doka. 1 2 3
|
|
|