A ran 12 ga wata, yayin da take yin shawarwari da jami'an Nijeriya, sakatariyar harkokin waje ta Amurka Hillary Clinton, wadda ke ziyara a nahiyar Afirka, ta mai da hankali sosai kan yanayin tsaro da ake ciki a muhimmin yankin fitar da man fetur na Nijeriya, wato yankin Neja Delta. Kuma ta bayyana cewa, rundunar sojan Amurka za ta ba da taimako wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki. Manazarta sun kyautata zaton cewa, Nijeriya wata muhimmiyar kasa ce a Afirka dake fitar da man fetur ga kasar Amurka. A sakamakon haka, ko shakka babu Amurka za ta mai da hankali kan illar da tashe-tashen hankali a Nijeriya za su yiwa aikin samar da man fetur.
A wannan rana, Hillary Clinton ta yi shawarwari da shugaban Nijeriya Umaru Yar'Adua, da ministan kula da harkokin waje na kasar Ojo Maduekwe, inda suka tabo magana kan yanayin tsaro da ake ciki a yankin Neja Delta, da batun yiwa tsarin zaben Nijeriya kwaskwarima, da kuma yadda za a iya yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka ci hanci da rashawa a kasar. A ciki, bangarorin biyu sun fi dora muhimmanci kan yanayin tsaro a yankin Neja Delta, sabo da yana da alaka da aikin samar da man fetur ga kasar Amurka.
1 2 3
|