Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-17 18:18:29    
Ganawa ta farko a tsakanin shugabannin kasashen BRIC

cri

A ran 16 ga wata a birnin Yekaterinburg na kasar Rasha, an gudanar da shawarwari a karo na farko a tsakanin shugabannin kasashe hudu da ake kira BRIC, wato Brazil da Rasha da Indiya da kuma Sin, wadanda tattalin arzikinsu ke bunkasa cikin sauri. A lokacin da ake fama da matsalar kudi a duniya, Sin da Rasha da Brazil da Indiya sun cimma daidaito ta fannin kara hada gwiwa da juna da tinkarar matsalar kudi ta duniya da farfado da tattalin arzikin duniya.

A cikin sanarwar da aka bayar bayan shawarwarin, kasashen hudu sun yi kira ga bangarori daban daban da su yi kokarin tabbatar da daidaiton da aka cimma a gun taron kolin G20 kan harkokin kudi da aka gudanar a watan Afrilu na shekarar da muke ciki. A game da batun gyaran hukumomin kudi na duniya da ke daukar hankalin bangarorin daban daban, kasashen hudu sun gabatar da cewa, kamata ya yi a daga matsayin kasashe masu tasowa da kuma kara wakilcinsu a cikin hukumomin kudi na duniya, sun kuma jaddada cewa, ya kamata a kafa tsarin harkokin kudi duniya mai inganci.

A mawuyacin halin da duniyarmu ke ciki ta fannin tattalin arziki, sauye-sauye na aukuwa ga yanayin siyasa na duniya. A cikin jawabinsa, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya ce, kamata ya yi kasashen hudu su kara amincewa da juna ta fuskar siyasa ta hanyar yin shawarwari da mu'amala da juna, sa'an nan, su yi amfani da fifikonsu ta fannonin albarkatun kasa da kasuwanni da kwadago da kimiyya da fasaha, don kara hadin gwiwa da juna ta fannin tattalin arziki. Bayan haka, ya kamata su kara mu'amala da juna a fannin al'adu, don aza harsashi mai karfi ga hadin gwiwarsu daga dukkan fannoni. Mr.Hu Jintao ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi kasashen hudu su nuna girmamawa ga juna wajen bin hanyarsu ta kansu, kuma su yi musanyar ra'ayoyi a kan kyawawan fasahohi na samun bunkasuwa.

1 2 3