Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-27 14:20:05    
Rangadin gani da ido a shahararren kauye mai samar da makamashi irin na halittu a Jamus

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, kauyen Juhnde na birnin Gottingen na jihar Niedersachsen ta kasar Jamus, wani kyakkyawan kauye ne dake da mutane sama da 700 kawai, amma ya yi suna sosai a kasar Jamus saboda shi ne kauye na farko mai samar da makamashi irin na halittu a kasar ta Jamus da ma Nahiyar Turai. A nan kauyen, mutane sukan mayar da wassu abubuwan bola-jari kamar na amfanin gona da kuma kashin dabbobi da dai sauran makamantansu don su zama makamashin lantarki da na zafi yayin da suke amfani da barbashin katako wajen dumama daki. Hakan ya biya bukatun mutanen kauyen na zaman yau da kullum.

A karshen shekarar 2004 ne aka soma gina kauye mai samar da makamashi irin na halittu bayan da aka zuba kudin Euro miliyan biyar da dubu dari biyu ta hanyar tattara kudade ,da samun kudin rangwame daga gwamnati da kuma rancen kudi daga banki.. Da farko, mutanen kauyen sun yi rajistar kafa wani hadadden kamfanin kauyen Juhnde, inda suka haka ramin gas da akan samu daga taki da kuma wata ma'aikatar samar da wutar lantarki. Ban da wannan kuma, kimanin kashi biyu bisa kashi hudu na mutanen kauyen sun yi kwaskwarima ko shimfida bututun samar da wutar lantarki da iska mai zafi da ruwan zafi a cikin gidajensu. Dadin dadewa, sun tattara wassu amfanin gona da kashin dabbobi don ruba su da ka iya zama gas. Daga baya dai, sun kona gas din don samun wutar lantarki da kuma makamashin zafi ,wanda suke iya yin afmani da su wajen dumama daki maimakon yin amfani da kwal da mai ko ma iskar gas a da.

1 2 3