Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 16:00:30    
Firaministan kasar Sin ya tashi zuwa kasar Masar don halartar taron ministoci tsakanin Sin da Afrika

cri

A ran 6 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya tashi zuwa kasar Masar don yin ziyara, kuma zai halarci bikin bude taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a kwana biyu masu zuwa a birnin Sharm El Sheikh. Firaministan kasar Sin ya kai ziyara a Afrika don ingiza hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika da kasar Masar da kuma kasashen Larabawa. A lokacin ziyararsa, Wen Jiabao zai gabatar da sabbin manufofin da aka tsara don kara hadin gwiwa da kasashen Afrika.

Babban aiki na ziyarar da Wen Jiabao zai yi shi ne halartar taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika. An fara yin dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a shekarar 2000, taron minitoci da aka kira a kowadanne shekaru 3 ya zama aiki mafi muhimmanci na dandanlin. A gun taron koli na Beijing na dandalin wato taron ministoci na 3 da aka yi a shekarar 2006, kasashen Sin da Afrika sun kafa sabuwar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. A lokacin da za a bude sabon taron ministoci, ministan ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Zhai Jun ya yi zance kan wannan taro.

1 2 3