Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-16 16:58:32    
Kungiyar kasashen 'yan-ba-ruwanmu tana zura ido wajen yin gyare-gyare da kanta da moriyar kasashe masu tasowa

cri

Ran 15 ga wata a birnin Sharm El Sheikh da ke bakin kogin Maliya na kasar Masar, an bude taron koli na kungiyar kasashen 'yan-ba-ruwanmu a karo na 15 wanda za a shafe kwanaki biyu ana yinsa. Masu bincike sun yi nuni da cewa, yadda kungiyar za ta sami sabon karfi, yadda za a iya kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da kuma yadda za a iya tinkarar manyan harkokin duniya za su zama muhimman batutuwan da za a tattaunawa cikin wannan taron koli.

An kafa kungiyar kasashen 'yan-ba-ruwanmu ta NAM ne a shekarar 1961. a wancan lokacin, akwai jayayya mai tsanani a tsakanin kasar Amurka da rukunin kasashen Soviet. Rikicin da ke tsakaninsu ya shafi kasashe kanana ko matsakaita, saboda haka, saboda haka, aka kafa wannan kungiyar, wannan ya nuna cewa, kasashe masu tasowa sun fara hada kansu domin samun bunkasuwa da kansu. Bayan da aka shiga karni na 21, an sami canje-canje sosai a fannonin siyasa, da tattalin arziki, kuma an sami sabannin ra'ayi cikin kungiyar NAM. A cikin sabon yanayin da ake ciki, ina makoma ta wannan kungiya?

Masu bincike suna ganin cewa, ka'idojin "'yancin kai, da mai cin gashin kai, da 'yan-ba-ruwanmu" da kungiyar NAM take tafiya yayin da aka kafa ta sun dace da yanayin da ake ciki a yanzu. Aiki mafi muhimmanci shi ne a bayyana sabuwar ma'anarsu, da nuna sabon karfi, da neman ci gaba bisa halin da ake ciki, da neman bunkasuwa tare, da kara yin hadin gwiwa, da moriyar juna.

1 2 3