Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-30 18:00:47    
Inganta huldodin kasashen Sin da Amurka ta fuskar cimma moriyar juna a karni na 21

cri

Kwanan baya, an kammala shawarwarin kasashen Sin da Amurka a zagaye na farko kan manyan tsare-tsare da harkokin tattalin arziki a Wangshinton D.C., hedkwatar kasar Amurka. A yayin taron yini biyu, jami'an kasashen biyu sun yi tattaunawar keke da keke kan muhimman batutuwan dake shafar bangarorin biyu, da shiyya-shiyya, gami da kasa da kasa. Hakan na nufin cewa, a halin da ake ciki yanzu, bangarorin Sin da Amurka suna kara cimma batun samun moriyar juna, da ci gaba da dogaro kan juna, wanda ke da babbar ma'ana ga tabbatar da bunkasuwar huldodin kasashen biyu mai dorewa.

An samu nasarori da dama a taron shawarwari a wannan gami. Alal misali, kasashen Sin da Amurka sun rattaba hannu kan takardar bayani game da karfafa hadin-gwiwa a fannonin sauyin yanayi, da harkokin makamashi da kiyaye muhalli, haka kuma bangarorin biyu sun amince da a maido da mu'amala da cudanya tsakanin sojojin kasashensu. A waje guda kuma, Sin da Amurka sun cimma daidaito kan batun tabbatar da dorewar kafofin hada-hadar kudi, da kara inganta mu'amala da hadin-gwiwa a harkokin kiwon lafiya.

1 2 3