Ran 1 ga wata rana ce ta cika shekaru 60 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, a sabili da haka, jama'a 'yan kabilu daban daban na kasar Sin sun gudanar da bukukuwa iri daban daban, domin yin murnar wannan ranar.
Jihar Guangxi mai cin gashin kanta ta kabilar Zhuang da ke kudancin kasar Sin jiha ce da ta fi yawan 'yan kananan kabilu a kasar Sin. Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, an sami manyan sauye-sauye a jihar Guangxi. A shekarar bara, yawan darajar kayayyakin da aka samar a jihar ya karu sau 120 bisa na shekarar 1950.
Domin nuna murnar cika shekaru 60 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, a ran 1 ga wata, a kauyuka 1041 na 'yan kakanan kabilu a duk fadin jihar, an daga tutar kasar Sin da kuma rera taken kasar, domin yin murnar ranar. A kauyen Minxing da ke birnin Guilin na jihar kuma, tsoffi da yara duk sun sanya tufafi masu kyau, domin yin murnar ranar.
1 2 3
|