Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-24 17:20:56    
Hu Jintao ya yi muhimmin jawabi a yayin babbar muhawara ta babban taron M.D.D. a karo na 64

cri

Ran 23 ga wata, a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, an kaddamar da babbar muhawara ta babban taron Majalisar Dinkin Duniya a karo na 64, inda kuma a cikin makon da muke ciki, shugabanni fiye da 140 na kasashen duniya suka yi shirin ba da jawabai kan inganta gudanar da harkoki a tsakanin mabambantan bangarori da yin tattaunawa a tsakanin al'adu daban daban da nufin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasuwa a duniya. A ranar farko ta babbar muhawarar, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ba da muhimmin jawabi.

Ali Abdussalam Treki, shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya a wannan karo ya yi jawabi da cewa, ba za a iya warware matsalolin da kasashen duniya ke fuskanta ba, har sai an inganta hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa. Daukar matakin gashin kai ba zai haifar da kome ba, sai ma ya tsananta rikici da kuma kawo cikas wajen neman samun hanyar warware lamura har abada. Ya kuma kara da cewa, babban taron Majalisar Dinkin Duniya a wannan karo zai mai da hankali a kan sauyawar yanayi da tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a Afirka da tabbatar da manufar samun bunkasuwa da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara a shekarar 2000, da sake shimfida zaman lafiya da kiyaye hakkokin dan Adam da aikin shimfida zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da dai saurunsu.

1 2 3