Ana ta kokarin tabbatar da siffar kasar Sin a kan matsayin wata babbar kasa dake sauke nauyin kanta A ranar 24 ga watan Satumba na shekarar 2008, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao da ya halarci taron M.D.D. a birnin New York, ya kira wani taron musamman a tsakaninsa da kwararru a fannonin tattalin arziki da kudi na kasar Amurka.
|
Saurin bunkasuwar da kasar Sin ta samu kan harkar zirga-zirgar jiragen sama da ta kumbuna Cikin shirin yau, zan yi muku bayani kan wasu nasarorin da sabuwar kasar Sin ta samu a fannin zirga-zirgar jiragen sama da ta kumbuna, bayan da aka kafa ta shekaru 60 da suka wuce.
|
Wasannin Olympics da ba za a iya mantuwa ba An haifi Zhao Ziao a sanyin safiyar ranar 8 ga watan Augustan shekarar 2008, daidai ranar da aka bude taron wasannin Olympics a Beijing, hakan ya sa ake kiran jariran da aka haifa a wannan rana da lakabin 'jariran Olympics'.Sai dai Li Yan, mamar Zhao Ziao, ta ce, da ma ba ta yi shirin haifar wata yarinya a shekarar 2008 ba, balle ma haifi diyarta a ranar da aka fara wasannin Olympics
|
Hanyar Li Qingming ta zuwa karatu Li Qingming, mai shekaru 16 da haihuwa, wani dan makarantar midil ne a birnin Baiyin na lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Yana zaune a kwarin babban tsauni. Kakanin-kakaninsa sun dade suna yin aikin gona, kuma iyalin Li Qingming na fama da talauci. Irin wannan mawuyancin halin da iyalinsa yake kasancewa ya kawo wa wannan yaro babban cikas wajen zuwa karatu.
|
Daga wayar tarho zuwa wayar salula, sannan yanar gizo, sauye-sauyen da ake samu kan tsarin sadarwa cikin shekaru 60 da suka gabata a kasar Sin Madam Lu Suiying, mai shekaru 59 da haihuwa, da iyalinta suna zaune a wani gidan da aka gina yau fiye da shekaru 100 da suka gabata a shiyyar Xicheng ta birnin Beijing. A cikin shirinmu na yau, bari mu shiga wannan gida, mu yi hira da madam Lu Suiying da iyalinta kan sauye-sauyen da aka samu a fannin sadarwa cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata a gidanta domin sanin sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a fannin fasahohin bayanai a cikin shekaru 60 da suka gabata bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin.
|
|