Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-27 16:41:16    
Kasar Sin za ta nuna manyan makamai masu linzami a bikin faretin sojoji a ran 1 ga watan Oktoba

cri
A kwanan baya, a lokacin da yake zantawa da manema labaru, Yu Jixun, mataimakin babban jagoran harkokin bikin faretin sojoji domin murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin kuma mataimakin kwamandan rundunar sojojin harba makamai masu linzami ta kasar Sin ya bayyana cewa, a ran 1 ga watan Oktoba, rundunar sojan makamai masu linzami za ta nuna makamai masu linzami mafi yawa kuma mafi yawan nau'o'i a tarihinta, za ta aika da bangarori 5 na sojojinta na harba makamai masu linzami. Haka kuma, a karo na farko za ta nuna makamai masu linzami da aka harba daga kasa da kuma sabon nau'in makamai masu linzami mai matsakaicin zango.

Ban da wannan kuma, a karo na farko sojojin harba makamai masu linzami dalibai za su shiga bikin faretin da kafarsu.

Yu Jixun ya kara da cewa, ana iya fahimtar ci gaban kasar Sin daga wajen bunkasuwar rundunar sojojin harba makamai masu linzami. Ya kuma ci gaba da cewa, har kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan bin manufar rashin daukar jagoranci wajen yin amfani da makaman nukiliya, da bin manyan tsare-tsare ta fuskar nukiliya domin tsaron kanta kawai. Haka kuma, ba ta yi shirin yin takara da saura a fannin makaman nukiliya ba. A matsayinta na wata babbar kasar da ke sauke nauyi a kanta, tabbas ne za ta taka rawa wajen samun zama lafiya da bunkasuwa a duniya.(Tasallah)