Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-10 20:23:13    
Ana ta kokarin tabbatar da siffar kasar Sin a kan matsayin wata babbar kasa dake sauke nauyin kanta

cri

A ranar 24 ga watan Satumba na shekarar 2008, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao da ya halarci taron M.D.D. a birnin New York, ya kira wani taron musamman a tsakaninsa da kwararru a fannonin tattalin arziki da kudi na kasar Amurka. Kan mawuyacin halin da ake ciki na fuskantar matsalar kudi ta duniya, Mr. Wen Jiabao ya ba da kwarin gwiwa ga mahalarta taron cewa, 'Amincewa ya fi muhimmanci bisa zinariya da kudi'. Kafofin watsa labaru na duniya sun bayar da labarai kan jawabin da Mr. Wen Jiabao ya yi, suna ganin cewa, wannan muhimmin ra'ayi ne da kasar Sin ke nunawa ta fuskar matsalar kudi. Yanzu kuma, shekara daya ta wuce, kasar Sin na kokari tare da kasashen duniya, don farfado da tattalin arziki na duniya, ta yadda ta samu girmamawa daga duniya. Mutane sun sha yin amfani da kalmomi a kan cewa 'Babbar kasa dake sauke nauyin dake kanta' da zummar tabbatar da rawar da kasar Sin ke takawa a dandalin kasashen duniya.

Daga wata kasa mai tsarin mulkin gurguzu da kasashen yamma suka yi mata kangiya, da nuna mata adawa a farkon lokacin kafuwar sabuwar kasar Sin, zuwa wata kasa mai sauke nauyin dake kanta a yanzu, kasar Sin ta bayar da taimako kan zaman lafiya da samun ci gaban duniya a shekaru 60 da suka wuce. Kalmomin 'Wata kasa mai sauke nauyin dake kanta' sun nuna canjawar da kasar Sin ta yi kan matsayinta, har ma sun nuna canjawar da kasashen duniya suka yi kan sanin rawar da kasar Sin ke takawa, da kuma matsayinta a dandalin kasashen duniya.
An kafa sabuwar kasar Sin ne a yanayin duniya na nuna adawa da juna tsakanin manyan rukunonin Tarayyar Soviet, da Amurka. Kan kangiya da barazana da kasashen yamma suka nuna mata, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan manufar harkokin waje ta zaman lafiya irin ta samun 'yancin kai. Ka'idojin zaman tare cikin lumana guda biyar, da manufar neman samun ra'ayoyi iri daya ba tare da yin la'akari da abubuwan da aka sha bambam a kansu ba da cimma daidaito ta hanyar yin shawarwari da kasar Sin ke gudanarwa sun samu goyon baya daga kasashen Asiya, da Afrika, da kuma Latin Amurka. A yanayin duniya na nuna adawa ga juna tsakanin manyan rukunoni guda biyu, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kan kafa tsarin duniya bisa adalci kamar yadda ya kamata.
1 2 3