Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-28 20:36:47    
Matsayin lafiyar jama'ar kasar Sin yana kan gaba a kasashe masu tasowa

cri

Ministan kiwon lafiya na kasar Sin Chen Zhu ya furta a ran 28 ga wata a nan birnin Beijing cewa, a cikin shakaru 60 bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, an kammala kafa tsarin ba da hidimar kiwon lafiya a birane da kauyuka, kuma an kyautata harkar kiwon lafiyar jama'a, matsayin lafiyar jama'ar Sin yana kan gaba idan aka kwatanta da sauran kasashe masu tasowa.

A gun taron manema labaru da aka yi, Chen Zhu ya bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar 2008, an kammala kafa tsarin ba da hidimar kiwon lafiya a birane da kauyuka. Bayan da aka fara yin gyare-gyare kan tsarin ba da tabbaci a fannin jiyya a shekaru 90 na karnin da ya wuce, yawan mutanen birane da nagaruruwa da suka ci gajiyar tsarin inshorar jiyya ya kai fiye da miliyan 300, kana manoma miliyan 833 sun ci gajiyar sabon tsarin ba da jiyya irin na hadin gwiwa, sabo da haka, yawan kudin da manoma suka kashe a fanin kiwon lafiya ya ragu sosai.

Bugu da kari, Chen Zhu ya ce, sakamakon kyautatuwar tsarin kiwon lafiya na kasar Sin, matsakaicin tsawon shekarun rayuwar mutane na kasar Sin ya karu daga 35 zuwa 73, yawan mutuwar mata masu ciki da jarirai ya ragu sosai. Matsayin lafiyar jama'ar kasar Sin yana kan gaba idan aka kwatanta shi da sauran kasashe masu tasowa.(Lami)