Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-01 14:55:50    
Sinawa na murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin

cri

Ran 1 ga watan Oktoba rana ce da ke cike da farin ciki ga jama'ar kasar Sin. A ran nan da safe, a babban filin Tian'anmen na birnin Beijing, an yi babban taron murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da bikin duba faretin soja. A wajen daya a sauran yankunan kasar Sin, mutane daga sassa daban daban sun gudanar da ayyukan taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin.

A jihar Tibet, a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, mutane sun yi kide-kide da wake-wake. Jama'a daga sassa daban daban na jihar Tibet suna ta shagalin tayar murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin.

A lardin Sichuan, wasu jama'a na yankin da aka hadu da abkuwar bala'in girgizar kasa suna ta kokari wajen sake gida da taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin da taya murnar bikin tsakiyar yanayin kaka. Mutane sun sa kyawawan tufafi, kuma suna amfani da tutar kasar da fitilu wajen yi wa gidaje ado.

A jihar Xinjiang mai ikon tafiyar da harkokin kanta, a ran 1 ga wata da safe, a filin birnin Urumci, an yi babban bikin daga tuta.

A ran 1 ga wata da safe, jama'ar yankunan Hongkong da Macau sun yi bikin daga tuta don taya murna, kuma wannan biki ya jawo hankalin mazauna yankunan.
Ba ma kawai a gidan kasar Sin ba, har ma masanan kimiyya na kasar Sin da ke a nahiyar kuryar duniya ta kudu da sojojin kasar da ke a Zirin tekun Aden sun taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin.

A ran 1 ga wata, a tashar bincike ta kasar Sin da ke a nahiyar kuriyar duniya ta kudu, masanan kimiyya sun yi bikin daga tuta, ban da haka kuma, a ran nan, an shirya liyafa taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, kuma an gayyaci masanan kimiyya da iyalinsu na kasashen waje da ke a nahiyar kuryar duniya ta kudu don halartar liyafar.A sa'i daya kuma, rukunin jiragen ruwan tsaro a karo na uku na jiragen ruwan sojan kasar Sin ya taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Manjo janar kuma mai ba da jagoranci na rukunin Wang Zhiguo ya ce, ko da yake rukunin jiragen ruwan tsaro yana yankin da ke da kilomita nisan fiye da dubu 10 daga kasar Sin, amma dukkan zukatan sojojin suna hade da jama'ar kasar Sin.(Abubakar)