Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-09 16:22:38    
Hanyar Li Qingming ta zuwa karatu

cri
Li Qingming, mai shekaru 16 da haihuwa, wani dan makarantar midil ne a birnin Baiyin na lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Yana zaune a kwarin babban tsauni. Kakanin-kakaninsa sun dade suna yin aikin gona, kuma iyalin Li Qingming na fama da talauci. Irin wannan mawuyancin halin da iyalinsa yake kasancewa ya kawo wa wannan yaro babban cikas wajen zuwa karatu. Yin karatu a makaranta ya zama babban burinsa, kuma ga alama, ba zai iya cimma burin nasa ba. Domin taimakawa 'yan uwansa wajen gama karatu, Li Qingming ya kusan gaza ci gaba da karatunsa. Duk da haka, wata manufar da aka soma aiwatar da ita yau da shekaru 3 da suka wuce ta ba shi taimako da yawa, ya samu damar ci gaba da karatunsa. Li Qingming ya ce,"Ba mu bukatar biyan kudin karatu da sauran tarkacen kudin makaranta, haka kuma, makarantarmu ta kan ba mu kudin alawus da yawansa ya kai kudin Sin yuan 70 ko fiye a ko wane wata. A matsayinmu na wadanda ke zaune a kauyuka, wannan na da matukar muhimmanci gare mu."

Irin wannan manufa ita ce soke kudin karatu da sauran tarkacen kudin makaranta da kuma ba da kudin alawus. Yau da shekaru da dama da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta soma gwaje-gwajen aiwatar da ita bi da bi a yankunan karkara. Wannan ya alamta cewa, an tabbatar da ba da ilmin tilas ba tare da biyan kudi ba a kauyukan kasar Sin. Wannan shi ne babban ci gaba da aka samu a fannin aiwatar da manufar ba da ilmin tilas a cikin shekaru 20 ko fiye da suka wuce.

Yau da shekaru 60 da suka wuce, wato a daidai lokacin kafuwar sabuwar kasar Sin, mutanen wannan kasa da yawansu ya wuce kashi 80 cikin dari bisa na duk fadin kasar suna da karancin ilmi. Kuma yawan yaran da suka shiga makarantar firamare bai wuce kashi 20 cikin dari kawai ba bisa jimilar yaran kasar Sin, kana kuma, yawan yaran da suka samu damar shiga makarantar midil bai wuce kashi 6 cikin dari kawai ba. Dan haka, tabbatar da ba da ilmin tilas a duk fadin kasar Sin muhimmin aiki ne a gun gwamnatin Sin a mabambantan zamani.

A shekarar 1986, kasar Sin ta kaddamar da dokar ba da ilmin tilas. A karo na farko ta hanyar kafa doka kasar Sin ta soma ba da ilmin tilas na tsawon shekaru 9, ta kuma tabbatar da hakkokin yara da matasa ta fuskar shiga makarantar firamare da ta midil. Daga baya kuma, kasar Sin ta samu saurin bunkasuwar ba da muhimmin ilmi?A karshen shekarar 2007, mutanen Sin da yawansu ya kai kashi 99.3 cikin dari sun samu ilmin tilas a duk fadin wannan kasa. A shekarar 2010, za a cimma burin ilmantar da dukkan mutanen Sin gaba daya.

Amma, kasar Sin wata kasa ce mai yawan mutane, ba ta da isasshen kudin ba da ilmin tilas, ta haka mutanen Sin na bukatar biyan wasu kudin karatu. Irin wannan kudi na matsayin babban nauyi ne ga dimbin iyalan da ke fama da talauci. Li Qingming ya fito daga daya daga cikin irin wadannan iyalai. A tunaninsa, a duk gabannin lokutan biyan kudin karatu, iyayensa su kan nuna damuwa ainun. Li Qingming ya ce,"Kafin gwamnatinmu ta soke kudin karatu da sauran nau'o'in kudin makaranta da kuma ba da kudin alawus, a ko wace shekara mu kan biya kudin karatu na yuan dari 4 ko fiye. Ta haka tare da kudin zaman rayuwarmu, mu kan kashe yuan dubu 1 ko fiye a ko wace shekara. Iyalina na fama da wahalar biyan kudin."

Domin tattara isasshen kudin karatu, iyayen Li Qingming sun sha tuna wata dabara, amma sau da yawa, Zhang Cui, mahaifiyar Li Qingming ta yi aniyar hana autarta Li Qingming ya ci gaba da karatu.

A daidai wannan lokaci, labari na farin ciki ya bazu. A lokacin kaka na shekarar 2006, wato a daidai farkon sabon zangon karatu, gwamnatin Sin ta soke kudin karatu da sauran nau'o'in kudin makaranta da kuma ba da kudin alawus ta fuskar zaman rayuwa a yankunan karkara.

Da jin wannan labari, Zhang Cui ta kasa gaskantawa. Bayan ta kidaya a tsanake, nan take damuwarta ta bace, sabo da a ko wace shekara, ta iya yin tsimin kudin karatu da yawansa ya kai yuan daruruwa, ta kuma iya samun kudin alawus na kusan yuan dari 9, autarta ya samu damar ci gaba da karatunsa. Ya zuwa yanzu, Zhang Cui ta yi zumudi sosai, inda ta ce,"Wannan manufar gwamnatin tamu ta rage mana nauyi. Muna yi farin ciki da wannan kyakkyawar manufa."

Li Qingming ya kwantar da hankalinsa nan da nan a yayin da ya san cewa, iyayensa ba za su ci gaba da damuwa kan kudin karatunsa ba. Ya kara samun maki mai kyau a sakamakon yin karatu cikin kwanciyar hankali. A makarantar midil ta Wuchuan a garin Li Qingming, da sauran 'yan makarantar fiye da 500 kamar Li Qingming su ma sun ci gajiya. Bisa adadin da ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta bayar, an ce, a shekarar 2007 kawai, 'yan makarantar firamare da ta midil kusan miliyan 150 da suke zaune a kauyuka sun ci gajiyar wannan manufa.

Baya ga yankunan karkara, tun daga watan Satumba na shekarar 2008, an fara soke sauran nau'o'in kudin makaranta a makarantar firamare da ta midil a biranen kasar Sin. Ana nan ana kafa tsarin jin dadin jama'a ta fuskar ba da ilmi a duk fadin kasar Sin.

A yanzu haka dai, Li Qingmin ya yi farin ciki sosai ba kawai domin samun damar yin karatu ba, har ma surar makarantar midil ta Wuchuan da yake karatu a ciki ta samu kyautatuwa kwarai. A sakamakon karin kudin da gwamnatin Sin take ta zubawa, babban ginin karatu ya maye gurbin azuzuwa marasa tsayi da aka yi da tabo. Li Qingming da abokan karatunsa sun samu sabbin teburori da kujeru. Kazalika kuma, injuna masu kwakwalwa sun shiga cikin zaman rayuwarsu, wadanda suke ganinsu ta talibijin kawai a da. Gao Bingwen, wani malamin makarantar midil ta Wuchuan ya yi murna ainun yana mai cewar,"Manufar gwamnatinmu ta soke kudin karatu da sauran nau'o'in kudin makaranta da kuma ba da kudin alawus ta sassauta matsin lambar da 'yan makaranta da suke zaune a kauyuka da kuma iyalansu suke fuskanta, ta kuma karfafa kuzarinsu da na iyayensu kan karatu. A sakamakon goyon baya daga gwamnatinmu, makarantarmu ta samu manyan sauye-sauye da kyautatuwa a fannoni daban daban, kamar kayayyaki da albarkatun malamai da kuma yanayin ba da ilmi."

Domin taimakawa karin 'yan makarantar da ke zaune a kauyuka su yi amfani da fitattun albarkatun ilmi, hukumar birnin Baiyin wato garin Li Qingming ta kebe kudin musamman domin gina wata sabuwar makarantar kwana, inda dubban yara za su fara sabon zangon karatu a wannan lokacin kaka.

Li Qingming ya bayyana cewa, ya taki sa'a, sabo da yana zama a zamani mai kyau. Wannan gaskiya ne. A cikin gajerun shekaru 60 da suka wuce, kasar Sin da ta taba fama da talauci ta zama babbar kasa ce ta fuskar ba da ilmi. Kokarinta na tabbatar da samun adalci a harkokin ba da ilmi ya taimakawa dimbin yara, kamar shi sauran yara su ma sun cimma burinsu na samun makoma mai kyau a sakamakon karatu.

To, bari mu nuna musu fatan alheri, muna fatan za su samu kyakkyawar makoma a nan gaba!(Tasallah)