A ran 27 ga wata, kafin ranar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin, gwamnatin Sin ta yi gagarumin bikin liyafa ga masana ilimi na kasashen ketare don murnar ranar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin a Beijing. Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma mataimakin firayim ministan Sin Li Keqiang ya halarci bikin, inda ya yi jawabi.
A farko dai, a madadin gwamnatin kasar Sin, da shugaban kasar Hu Jintao, da kuma firayim ministan Sin Wen Jiabao, Li Keqiang ya yi gaisuwa da kuma nuna godiya ga dukkan masana ilimin kasashen ketare sakamakon suke mai da hankali da nuna goyon baya da suke yi da kuma shiga ayyukan raya kasar Sin.
Bugu da kari, mista Li ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da kara yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, da kuma tsayawa tsayin daka kan gudanar da manyan tsare-tsare na yin amfani da kwararru don kara raya kasa, da kiyaye ikon mallakar ilimi, kana da yin kokarin shigo da masana ilimi na kasashen ketare, don kara yin mu'amala da hadin gwiwa da kasa da kasa a fannoni mafi yawa, ta yadda za a ba da taimako ga bunkasuwar kasar Sin ta hanyar zamani, da raya duk duniya cikin lumana.(Asabe)
|