Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-02 16:18:06    
Kafofin sadarwa na yankunan Hongkong da Macau sun bayar da labari a game da bukukuwan murnar cika shekaru 60 kafuwar sabuwar kasar Sin

cri

A ran 2 ga wata, kafofin yada labaru na yankunan Hongkong da Macau sun bayar da labarin a game da bukukuwan murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin da aka yi a birnin Beijing a ran 1 ga wata, kuma sun nuna babban yabo ga sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 60 da suka wuce.

Jaridar Takungpao ta yankin Hongkong ta bayar da labarin cewa, bukukuwan murnar cika shekaru 60 kafuwar sabuwar kasar Sin sun bayyana karfin tasiri a duniya, kuma kasar Sin ta samu sabon kwarjini a duniya. Jaridar Mingpao ta yankin Hongkong ta fitar da sharhin da ke cewa, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi jawabin cewar kasar za ta tsaya tsayin da ka kan manufar kasa daya mai tsarin mulki iri biyu da kiyaye bunkasuwar yankunan Hongkong da Macau a cikin dogon lokaci, wannan ya shaida cewar kasar Sin tana mai da hankali sosai a kan yankunan Hongkong da Macau. Yayin da jaridar Shimindaily ta Macau ta bayar da labarin game da bikin faretin soja, ta bayar da sharhi cewa, wannan faretin soja a karo na farko a cikin 'yan shekaru 10 da suka wuce, kuma ana iya sheda karfin sojan kasar Sin da sakamakon da kasar ta samu a cikin 'yan shekaru da suka wuce.(Abubakar)