Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-28 10:07:20    
Gidan radiyon kasar Sin zai gabatar da shirye-shiryen murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin kai tsaye ta hanyoyi biyar

cri
A ran 1 ga watan Oktoba, a filin Tian Anmen na birnin Beijing, bangarori daban daban na babban birnin kasar Sin za su yi gagarumin bikin murnar ranar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, da bikin faretin soja da na fararen hula. A wannan lokaci, gidan radiyon kasar Sin zai watsa shirye-shiryen bukukuwa kai tsaye ta hanyoyi biyar wato watsa shirye-shirye dangane da bukukuwa ga kasashen ketare da gida, da kuma watsa shirye-shirye ta hanyar bidiyo da hotuna na Internet da dai sauransu, ta yadda za a watsa shirye-shiryen bukukuwa daga dukkan fannoni.

Sassan harsuna 26 na gidan radiyon kasar Sin kamarsu sashen Sinanci, da Turanci, da harshen Mongoliya, da kuma na Korea da dai sauransu za su watsa shirye-shiryen bukukuwa kai tsaye. Wannan shi ne babban aikin watsa shirye-shirye kai tsaye da gidan radiyon kasar Sin ya shirya ta harsuna mafi yawa. A sa'I daya kuma, rassa 27 na CRI dake kasashen ketare da gidajen radiyon kasashen ketare fiye da 150 da ke hada kai da CRI za su watsa shirye-shiryen bikin kai tsaye. Ban da haka kuma, sassan harsuna 26 kamar su Sinanci, da Turanci, da na harshen Rasha, da Faransanci, da Larabci da dai sauransu za su watsa shirye-shiryen ta hanyar bidiyo da hotuna na Internet.(Asabe)