A ran 27 ga wata, Mr. Liu Peng, shugaban babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin shekaru 60 da suka gabata bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, kasar Sin ta samu ci gaba sosai a fannonin motsa jikin jama'a da na yin gasa, kuma ta samu babban ci gaban da ke jawo hankalin kasashen duniya.
A yayin taron manema labaru da ofishin yada labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya, Mr. Liu Peng ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu yawan filaye da dakunan motsa jiki iri iri ya kai fiye da dubu 850, wato ya ninka sau 200 ko fiye bisa na farkon lokacin kafuwar sabuwar kasar Sin yau shekaru 60 da suka gabata. A waje daya, yawan mutanen da su kan motsa jiki ya kai kusan kashi 30 cikin kashi dari bisa na jimillar mutanen kasar. Bugu da kari kuma, kasar Sin ta kuma samu sakamako mai kyau wajen wasannin motsa jiki na yin gasa. Ya zuwa watan Agusta na shekara ta 2009, yawan zakarun da kasar Sin ta fitar a fannin wasannin motsa jiki a duniya ya kai fiye da 2300, kuma sun kafa sabbin matsayin bajimta na duniya kusan sau 1200. (Sanusi Chen)
|