Za a gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin a ranar 1 ga wata mai zuwa a Beijing. A halin yanzu, ma'aikatu kamar suna kula da yanayi, da tafiye-tafiye, da kiwon lafiya, da kuma tsaro sun riga sun dauki matakai musamman don tabbatar da yin bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin cikin lumana.
A ran 1 ga wata da safe, za a yi gagarumin bikin faretin soja da na fararen hula a filin Tian Anmen na Beijing. Kuma da daddare, za a yi shagulgulan jama'a.
Ban da haka kuma, ma'aikatar kula da harkokin yanayi ta kasar Sin ta shiga yanayin musamman na ba da hidimar harkokin yanayi, don mai da hankali kan sauyin yanayin da zai kawo tasiri ga bikin.
Bugu da kari, don hana yaduwar cutar mura mai nau'in A(H1N1), ma'aikatar kiwon lafiya da rigakafin cututtuka ta kasar Sin tana shirya yin allurar rigakafi ga yawancin mutane da daliban da za su shiga bukukuwan.
Ban da wannan kuma, an kaddamar da aikin tsaro a duk fannoni.(Asabe)
|