Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-01 21:52:30    
Jama'r Sin sun yi bikin murnar cikar shekaru 60 da kafuwar kasar Sin a filin Tian'anmen

cri

A ran 1 ga wata da karfe 8 na dare, an yi bikin murnar cikar shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin a filin Tian'anmen na birnin Beijing, kuma jama'a kusan dubu 60 sun halarci bikin. Shugabannin kasar Sin da na JKS da kuma wakilai na sassa daban daban sun hau ginin Tian'anmen domin kallon gagarumin bikin tare da jama'a.

Tare da waka mai dadin ji da ke da taken "mahaifiya kasata", an kaddamar da shagalin murnar cika shekaru 60 da kafuwar kasar Sin. Sakamakon wasan wuta da aka yi da ke da sifar lamba 60, nan da nan halin annashuwa ya game a ko ina a filin Tian'anmen.

Kuma a cibiyar filin, ana iya gain cewa, 'yan wasa fiye da 4000 suna yin kwalliya kamar itatuwa masu ba da haske, daga baya kuma sun nuna zane-zane 865 da ke da halin musamman na kasar Sin kamar babbar ganuwa da kuma sakar gargajiya ta Sin da ake kiranta Zhongguojie.

Ban da wannan kuma a filin Tian'anmen da kuma titin Chang'an, ana iya ganin cewa, dimbin mutane suna raye-raye da suka tsara da kansu. Kamar jama'a na unguwar Dongcheng ta Beijing suna raye-raye tare da sojoji domin nuna jituwa da ke tsakanin fararen hula da sojoji. Dalibai kuma suna yin raye-rayen zamani domin nuna kuruciyarsu. Haka kuma manoma suna raye-raye domin nuna halin da sabbin yankunan karkara ke ciki.