Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-10 17:38:30    
Wasannin Olympics da ba za a iya mantuwa ba

cri

An haifi Zhao Ziao a sanyin safiyar ranar 8 ga watan Augustan shekarar 2008, daidai ranar da aka bude taron wasannin Olympics a Beijing, hakan ya sa ake kiran jariran da aka haifa a wannan rana da lakabin 'jariran Olympics'.Sai dai Li Yan, mamar Zhao Ziao, ta ce, da ma ba ta yi shirin haifar wata yarinya a shekarar 2008 ba, balle ma haifi diyarta a ranar da aka fara wasannin Olympics. Da ma likita ya duba jikinta, ya ce za ta haifu a ranar 3 ga watan Augusta, hakan ya sa abokanta suka bayyana fatan cewa, watakila za a haifi wani 'yaron Olympics', idan za a dage lokacin kadan. A karshe dai, an haifi Zhao Ziao a ranar 8 ga watan Augusta kamar yadda aka yi bukata, wannan ya sa mamar yarinyar ta ga wata alakar da ta hada diyarta da wasanin Olympics, shi ya sa ta rada mata sunan 'Ziao', wato yarinyar da iyayenta za su yi alfahari da ita, haka kuma sunan na da ma'anar ''yar Olympics'.

'Ao ya yi kama da O na Olympics, sa'an nan na rubuta shi kamar Ao da ke da ma'anar alfahari, don nuna fatana cewa, za ta zama wata yarinyar da za mu yi alfahari da ita. Haka kuma, ma iya cewa ma'anar suna 'yar Olympics ke nan, domin Allah ya huwace mata wata alaka da wasannin Olympics, shi ya sa na rada mata sunan, don tunawa da wasannin Olympics da aka yi a Beijing.'

Zuwa yanzu, shekara daya ta wuce, Zhao Ziao ta riga ta samu fasahar tafiya da hannu da kafa, da kuma tashi tsaye. Duk da cewa ba ta iya magana ba tukuna, amma ta iya mu'amala da iyayenta ta idanu da hannu. Lokacin da aka yi bikin ranar haihuwarta na rabin shekara, Li Yan da mijinta sun kai diyarsu wurin da aka shirya wasannin Olympics na Beijing, wato babban filin wasa na 'shekar tsuntsu'.

'Mun gaya mata cewa, lokacin da aka haife ki, an shirya wani gagarumin biki a nan don kaddamar da taron wasannin Olympics. Bayan da ki yi girma a nan gaba, za mu kai ki wurin don mu yi kallon sauran gasannin wasa. A lokacin da muka yi zancen, ta daga kai ta saurari maganarmu sosai. '

Li Yan ta ce, tana fatan cewa ranar da aka haifi Ziao za ta kawo mata abubuwa da yawa, ba sanin wasan Olympics kawai ba, har ma za ta sa ta fahimci abubuwa masu ban sha'awa da ke cikin wasannin motsa jiki, sa'an nan ta sa ta fahimci muhimmancin bunkasa jiki. Ra'ayin Li Yan ya zo daya da na sauran mazauna birnin Beijing da yawa. A hakika, bayan wasannin Olympics, ra'ayin jama'ar birnin Beijing dangane da halartar wasannin motsa jiki ya sauya sannu a hankali. Haka kuma, bayan wasannin Olympics an bude kofar dakin wasanni ga jama'a, ta yadda aka samar musu da wuraren motsa jiki da yawa. Zhang Chonglu, wani dattijon da ke da shekaru 72 a duniya, ya zaune a dab da dakin wasan ninkaya na 'water cubic', inda aka shirya wasannin iyo na Olympics a shekarar 2008. Shi ya sa, a watan Yunin shekarar bana, da aka bude dakin ke da wuya, Zhang ya je iyo a wurin tare da jikansa, ya ce,

'Na zo da jikana domin mu duba yadda wurin yake. Ga shi ginin ya yi girma, sa'an nan akwai kayayyaki masu ci gaba. 'Yan wasan kasarmu sun samu lambobi da yawa a nan. Gaskiya kowa na son zuwan wurin don bude ido.'

Haka kuma, Zhang Mingyang, jikan Zhang Chonglu, wanda ke da shekaru 13 da haihuwa, ya yarda da ra'ayin kakansa, inda ya ce, bude kofar dakin wasannin Olympics ga jama'a zai sa mazauna Beijing su kara halartar cikin wasan motsa jiki.

'Dalilin da ya sa aka kafa dakin wasa shi ne domin samarwa mutane da wani filin, inda za su iya motsa jikunansu. Abin na da kyau, da aka samu damar motsa jiki tare. Wannan daki aka yi amfani da shi ne a lokacin wasannin Olympics, 'yan wasan ninkaya masu kwarewa da yawa sun taba iya a ciki. Tabban ne akwai kayayyaki masu ci gaba a ciki. Shi ne ya sa na zo wurin don kashe kwarkwatar ido.'

1 2