Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-01 21:56:10    
An yi murnar cikar shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin

cri

Ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. A sassa daban daban na wannan kasa, an yi murnar wannan muhimmiyar rana ta mabambantan hanyoyi.

Ran 1 ga watan Oktoba da karfe 10 na safe, a babban filin Tian'anmen da ke nan birnin Beijing, an yi babban taron murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi wani muhimmin jawabi, inda ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da bin manufar gurguzu mai halin musamman, za ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, za ta sa kaimi kan raya kanta ta hanyar kimiyya da raya zaman al'umma mai jituwa kuma mai matsakaicin karfi. Kana kuma, kasar Sin za ta inganta hadin gwiwar abokantaka da dukkan kasashen duniya, za ta sa kaimi kan bunkasa duniya mai jituwa. Dadin dadawa kuma, shugaba Hu ya ce, jama'ar Sin na da karfin zuciya da kwarewa wajen raya kasarsu yadda ya kamata, kana haka suke a fannin bai wa kasashen duniya gudummawarsu.

A yayin bikin duba faretin soja da aka yi bayan jawabin shugaban Hu,rukunnoni 56 na rundunar sojan kasar Sin sun nuna sabon sakamakon da Sin ta samu a fannin aikin soja. Bayan bikin duba faretin soja, fararen hula daga sassa daban daban dubu 100 da motoci 60 masu launuka daban daban sun yi kasaitaccen maci cikin fara'a a filin Tian'anmen

Misalin karfe 8 na dare na wannan rana, an yi shagalin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin a filin Tian'anmen, mutane kimanin dubu 60 sun nuna wasanni a gun shagalin. Hu Jintao da sauran jami'an jam'iyyar kwaminis ta Sin da na gwamnatin kasar sun halarci wajen shagalin.

Kazalika kuma, yau a sauran sassa daban daban na kasar Sin, an shirya mabambantan harkoki domin murnar cikar shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. (Tasallah)