Ran 27 ga wata, manema labaru 89 daga kasashe ko yankuna 53 na Asiya, da Afirka, da Latin Amurka sun sauka birnin Beijing, wadannan manema labaru daga kasashe masu tasowa za su ba da rahotanni kan ayyukan bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin.
A wannan rana da yamma, manema labaru sun kai ziyara ga cibiyar watsa labaru ta bikin. Kafin wannan kuma, yawancinsu sun riga sun kai ziyara ga birnin Shanghai, da lardin Jiangsu, da lardin Guangdong. A wannan rana, mataimakin babban edita na jaridar Al Ahram ta kasar Masar ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana bunkasuwa cikin sauri sosai, haka ma a aikin gona, da masana'antu da sauran fannoni, kasar Sin ta samu ci gaban da ke jawo hankalin kasashen duniya sosai.
Manema labaru sun nuna cewa, bunkasuwar kasar Sin tana hade da moriyar kasashe daban daban, kuma suna fatan kasar Sin za ta samu ci gaba ma fi kyau a nan gaba. [Musa Guo]
|