Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-29 14:00:28    
Radiyon kasar Sin CRI zai yi amfani da shafunan Internet na harsuna da yawa don watsa shirye-shiryen bidiyo game da bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin kai tsaye

cri
A ranar 1 ga watan Oktoba, kungiyoyi daban daban na babban birnin kasar Sin za su yi gagarumin bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin da bikin faretin soja da na fararen hula a filin Tian Anmen na Beijing, kuma da dare za a gudanar da sauran shagulgulan jama'a. A wancan lokaci, gidan radiyon kasar Sin zai watsa shirye-shiryen bidiyo na bikin ta shafunan Internet na harsuna da yawa.

An ba da labari cewa, a ran 1 ga watan Oktoba, sassan harsuna goma kamarsu Sinanci, da Turanci, da harshen Japan, da na Korea, da na Vietnam, da Larabci, da na Rasha, da na Spanya, da kuma Faransanci, gami da Jamusanci za su watsa shirye-shiryen bidiyo ta Internet. Ban da haka kuma, sassan harsuna biyar wato Turanci, da harshen Mongoliya, da na Spanya, da kuma Faransanci, gami da Jamusanci za su watsa shirye-shiryen bidiyo na shagulgulan dare ta Internet a ran nan da dare.

A lokacin, dukkan jama'a masu sauraro dake yin amfani da wadannan harsuna za su iya duba bikin ta Internet. Shirye-shiryen da za a watsa a ranar za su fara ne daga karfe 9 da mintoci 45 na agogon Beijing, kuma shirye-shiryen da za a watsa a dare za su fara daga karfe bakwai da mintoci 45 har zuwa karewar bikin.(Asabe)