A ran 1 ga wata da misalin karfe 8 na dare, an yi shagalin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin a filin Tian'anmen, mutane kimanin dubu 60 sun nuna wasanni a gun shagalin. Hu Jintao da sauran jami'an jam'iyyar kwaminis ta Sin da na gwamnatin kasar sun halarci wajen shagalin. (Lami)
|