Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-27 17:25:12    
An wallafa littafi "Shekaru 60 da suka gabata bayan kafuwar sabuwar kasar Sin"

cri
A ran 26 ga wata, an wallafa littafi mai suna "Shekaru 60 da suka gabata bayan kafuwar sabuwar kasar Sin" a nan birnin Beijing. Wannan littafi ne da ke kunshe da bayanan tarihi da yawa. Kuma Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya rubuta wani bayanin gabatarwa domin wannan littafi.

A cikin bayaninsa, Mr. Wen ya nuna cewa, bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jama'ar kabilu daban daban na kasar sun hada kan juna kuma sun yi kokari sosai. Sabo da haka, kasar Sin ta samu ci gaban da ke jawo hankalin sauran kasashen duniya kwarai, kuma ta kama kan hanyar gurguzu ta musamman da ke dacewa da halin da kasar Sin ke ciki. Yanzu, kasar Sin wadda ke bin tunanin gurguzu, kuma ke kokarin zamanintar da kanta da fuskantar da duk duniya da kuma ke fuskantar da nan gaba tana kasancewa a gabashin duniya. (Sanusi Chen)