Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-10 17:40:30    
Saurin bunkasuwar da kasar Sin ta samu kan harkar zirga-zirgar jiragen sama da ta kumbuna

cri

Cikin shirin yau, zan yi muku bayani kan wasu nasarorin da sabuwar kasar Sin ta samu a fannin zirga-zirgar jiragen sama da ta kumbuna, bayan da aka kafa ta shekaru 60 da suka wuce.

'Na riga na fito daga kumbon Shenzhou na 7, ina lafiya kalau. Sa'an nan ina gaisuwa ga jama'ar kasar Sin da ta duk duniya.'

A ranar 27 ga watan Satumba na shekarar 2008, Zhai Zhigang, dan sama jannatin kasar Sin, ya yi tafiya a sararin samaniya da ke da tazarar kilomita 300 da wani abu zuwa kasa, wanda ya zama basine na farko da ya yi tafiyar. Muryar da muka ji ita ce yadda ya yi gaisuwa zuwa ga jama'ar kasar Sin da ta duk duniya a can sararin samaniya. Abin da ke da ma'anar tarihi yana alamantar cewa, kasar Sin ta zama kasa ta 3 wadda ke mallakar fasahar fito da dan sama jannti daga kumbo, a biyo bayan kasashen Rasha da Amurka.

Fasahar daukar mutane zuwa sararin samaniya da kumbo ta hada ilimi da yawa a waje daya, wadda ta shafi roka, da kumbo, da kayan sadarwa, da dai sauran na'urori da yawa. Abin da ya sa ta zama wani aikin da ya fi girma, da sarkakkiya, da kuma fi zame mana kasada. Zhang Jianqi, mataimakin babban darekata mai kula da aikin daukan mutane zuwa sararin samaniya da kumbo na kasar Sin, ya ce, ba zai yiwu ba a fitar da dan sama jannati daga kumbo, in ba tare da fasaha ta ci gaba sosai ba.

'Abin yana bukatar mu samu ci gaba a fasahohi da yawa, kamarsu fasahar sarrafa yanayin iskar dake cikin kumbo, da fasahar kera tufafin musamman da ake sawa a sararin samaniya, da kuma fasaha dangane da na'urori da kayayyaki, da dai makamantansu.'

Sai dai abin da aka samu yanzu ya kasance wani buri ne na jama'ar kasar Sin kawai shekaru 60 da suka wuce. Domin a lokacin, kasar Sin ba ta da roka, balle ma masanan kimiyya da ke da fasahohi na ci gaba. A hakika, yawan mutane masu binciken kimiyya da fasaha na kasar Sin bai kai 500 ba a lokacin.

1 2 3