Bisa rahoton da hukumar kididdigar ta kasar Sin ta bayar a ran 28 ga wata, an ce a farkon shekaru 80 na karni na 20, yawan kudin da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen yaki da gurbatar muhalli ya kai kashi 0.51 cikin kashi 100 na GDP, kana a shekarar 2008, yawan kudin da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen yaki da gurbatar muhalli ya kai kashi 1.49 cikin kashi 100 na GDP.
A cikin rahoton, an ce, cikin shekaru 60 da suka wuce bayan da aka kafa sabuwar gwamnatin Sin, musamman tun bayan gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare, ana inganta aikin kiyaye muhallin halittu. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a farkon shekaru tamanin na karni na 20, yawan kudin da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen kiyaye muhalli ya wuce kudin Sin biliyan 2, a shekarar 2008, yawan kudin da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen kiyaye muhalli ya kai kudin Sin biliyan 449.
A cikin rahoton, an ce, aikin kiyaye muhalli a kasar Sin ya samu bunkasuwa sosai. Matakan watsa labarun muhalli a fili, da yin kira ga jama'a da su shiga aikin kiyaye muhalli, da bude taron sauraron shaida, da duba jami'ai a fannin kiyaye muhalli sun shiga babbar manufa bi da bi.Abubakar)
|