Bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin yana tafe, a ran 28 ga wata, Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin ya shugabanci taron majalisar gudanarwa da aka saba yi domin shisshirya ayyukan bikin taya murnar kafuwar sabuwar kasar Sin.
A yayin wannan taro, an yi nuni da cewa, a gun bikin, za a yi ayyukan taya murna a jere. Kuma bikin zai zo ne a tsakar lokacin kaka, dole ne a daidaita ayyuka daban daban a lokacin bikin tayar murnar kafuwar sabuwar kasar Sin da ayyukan samar da kayayyaki da zaman rayuwar jama'a, tare da rika inganta tsarin zaman al'umma, domin tabbatar da yin bikin cikin farin ciki da lunama.
A ran 1 ga watan Oktoba, za a yi bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin a filin Tian'anmen na Beijing tare da bikin faretin sojoji, kuma jama'a za su yi maci cikin fara'a. Rediyon kasar Sin wato CRI zai watsa yanayin bikin kai tsaye ta kafofin rediyo da Internet cikin harsuna 26.
Ban da haka kuma, 'yan jarida 89 daga kasashe da yankuna 53 na Asiya, da Afirka, da Latin Amurka sun sauka a birnin Beijing a kwanakin baya, za su aika da rahotanni kan bikin tayar murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin. [Musa Guo]
|