in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna goyon baya ga kasar Saliyo wajen yaki da cutar Ebola
2014-08-18 15:29:53 cri
Jakadan Sin dake kasar Saliyo Zhao Yanbo ya bayyana a ranar 17 ga wata cewa, kasar Sin ta nuna goyon baya ga kasar Saliyo wajen yaki da cutar Ebola.

A ranar 11 ga wata ne kayayyakin jin kai da kasar Sin ta samar wa kasar Saliyo suka isa birnin Freetow, yayin da tawagar masanan kiwon lafiya da ta likitoci na kasar Sin suka isa kasar Saliyo a ranar 12 da kuma 17 ga wata.

Ban da wannan kuma, Zhao Yanbo ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Saliyo ta riga ta raba kayayyakin taimako a asibitocin kasar, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar Ebola. Haka kuma jami'an gwamnatin kasar sun nuna yabo ga taimakon na kasar Sin, in ji jakadan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China