Hukumar WHO ta ce, halin da ake ciki a birnin Ikko, inda nan ne cutar ta fara bulla a Nigeria a watan Yuli, ya nuna cewa, akwai alamun nasara, domin a yanzu masu jiyyar cutar wanda aka tabbatar suna dauke da cutar ta Ebola, dukansu cutar ta kama su ne daga tushe guda.
Hukumar ta ce, kawo ya zuwa yanzu, binciken jama'ar da ake yi wadanda suka yi hulda da wadanda suka kamu da cutar bai gano wasu mutane dauke da cutar ba daga wani tushe na dabam, in ban da tushen farko wanda shi ne asalin yaduwar cutar a Nigeria.
Haka zalika hukumar WHO ta ce, yanayin cutar a kasar Guinea, inda cutar ta fara bulla a yammacin Africa a watan Disambar bara, ya nuna akwai alamun sauki, to amma hukumar ta ce, a kasashen Liberia da Saliyo akwai fargaba a game da yaduwar cutar.
To amma MDD tayi gargadin cewa, wannan ba wai yana nufin cewar an murkushe cutar ba a Guinea, domin ko a kwanan nan an samu bullar cutar a wasu wurare da a da babu cutar. (Suwaiba)