in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan kasar Sin sun horar da likitocin kasar Saliyo dake bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar Ebola
2014-08-15 15:53:42 cri
A ranar 14 ga wata a birnin Freetow na kasar Saliyo, tawagar masanan kiwon lafiya na kasar Sin dake ba da tallafi a kasar ta shirya kwas din horar da likitoci fiye da 20 dake bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar Ebola. Inda mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Saliyo Abu Forfana ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da ta aikewa da kayayyakin taimako ta jirgin saman musamman ga kasarsa, kana yana fatan likitocin za su yi amfani da wannan damar samun horaswa wajen koyon yadda za a yi amfani da na'urori da sauran kayayyakin taimako yadda ya kamata.

Mai bada shawara a sashen harkokin ciniki na ofishin jakadancin Sin dake kasar Saliyo Zou Xiaoming ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun damu sosai kan cutar Ebola da ya afkawa kasar Saliyo, kuma yana fatan taimakon da tawagar masanan Sin suka bada da kayayyakin da aka samar za su bada kariya ga likitoci yayin da suke bada jinya ga masu kamu da cutar Ebola, da taimakawa kasar wajen kawar da cutar cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China