Tawagar masanan kiwon lafiyar kasar Sin mai kunshe da mutane 3, ta isa birnin Freetown hedkwatar kasar Saliyo a daren ran 12 ga wata.
Wannan ne karo na farko da Sin ta tura tawagar masanan kiwon lafiyar ta zuwa kasashen waje, ciki hadda tawagogi uku da suka nufi kasar Guinea, da Saliyo da kuma Laberiya, kowacensu kunshe da masana 3.
An bayyana cewa kowace tawaga na kunshe da masanin cututtuka masu yaduwa guda, da kuma masanan kashe kwayoyin cuta biyu.
A daya hannun, kayayyakin tallafin da Sin ta aike da su a karo na biyu zuwa gwamnatin Saliyo domin tinkarar cutar Ebola sun isa kasar da yammacin ran 11 ga watan nan. (Amina)