Kakakin hukumar Gregory Hartl ya yi matukar godiya ga kasar Sin don karin taimakon kayayyakin agaji da masanan kiwon lafiya da ta tura wa kasashen Afirka a wannan lokaci. Ya ce, fasahohin kasar Sin kan yadda za a iya ba da taimako ga al'ummomin yankin, da kuma hana yaduwar cutar yadda ya kamata suna da muhimmiyar ma'ana ga kasashen da cutar ta shafa a halin yanzu.
Bugu da kari, mataimakin babban sakataren WHO Keiji Fukuda ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai kan harkokin kiwon lafiya, lamarin da ya sa ta samu kyakyyawan sakamako kan harkokin binciken cututtuka, samar da labaran da abin ya shafa yadda ya kamata da dai sauransu. Don gane haka, yammacin kasashen nahiyar Afirka suke iya yin koyi daga kasar Sin, kara zuba jari kan ayyukan kiwon lafiya, wanda zai ba da muhimmin taimako ga kasashen wajen yaki da cutar Ebola wadda a halin yanzu, ta riga ta kasance hadarin kiwon lafiya na gaggawa dake janyo hankulan kasa da kasa. (Maryam)