in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO na duba yiwuwar samar da magani da alluran rigakafin cutar Ebola
2014-08-22 14:17:37 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, za ta gudanar da wata tattaunawa a babban ofishinta dake Geneva, a kan yiwuwar samar da magani da allurar rigakafin cutar Ebola.

Hukumar lafiyar ta ce, an shirya taron, da zimmar tattara kwararru domin samar da kulawa ta magani da allurar rigakafi ta hanyar gwaje-gwaje wadanda za su yi tasiri a kan cutar ta Ebola, taron zai kuma tattauna rawar da kwararru za su taka a wajen dakile yaduwar cutar Ebola, a Afrika ta yamma.

Kwararru na duniya fiye da dari da ake sa ran za su halarci taron, ciki har da masu bincike domin harhada magunguna da kwararru kusan 20 daga Afrika ta yamma.

Hakazalika taron zai duba batutuwan da suka shafi samar da magunguna bisa la'akari da bin ka'ida, tare da bin tsarin dokokin da suka dace, za kuma a duba maganar samar da magani da zai yi tasiri, ba tare da haddasa wata matsala ba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China