in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD kan cutar Ebola na ziyarar aiki a yammacin Afrika
2014-08-22 10:02:05 cri

Jami'in MDD kan cutar Ebola, David Nabarro, ya isa a ranar Alhamis a Monrovia, babban birnin kasar Liberiya a wani zangon farko na rangadinsa a cikin kasashen yammacin Afrika hudu da annobar cutar Ebola ta fi shafa.

Shugabar tawagar MDD a Liberiya (MINUL), madam Karin Landgren ta bayyana cewa, wannan ziyara na jaddada babbar niyyar MDD ta kokarin kawar da cutar Ebola.

Tawagar MINUL ta kebe wani bangaren ayyukanta domin tallafawa gwamnatin Liberiya kan kokarin da take na yaki da cutar Ebola.

Madam Landgren ta jaddada cewa, illar wannan cuta ba ta tsaya ga mutanen da suka kamu ba, har ma bala'inta ya shafi iyalansu da al'ummominsu. Kuma cutar ta kasance wata babbar barazana ga kiwon lafiya, tsaron abinci da tattalin arzikin kasar Liberiya.

A cewar wasu alkaluman hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, tsakanin ranakun 17 da 18 ga watan Agustan shekarar 2014, an gano wasu sabbin mutane 221 da suke dauke da cutar Ebola ko ake zaton suna dauke da wannan cuta, haka kuma an tabbatar da mutuwar mutane 106 a kasashen Guinee, Liberiya, Nijeriya da Saliyo. A halin yanzu, a dunkule adadin mutanen da suka kamu cutar Ebola ya kai 2.473, daga ciki, mutane 1.350 suka mutu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China