Bisa sabon rahoton da hukumar ta fitar, an ce, ta samu wasu rahotanni cewa, an gano wasu da ake zaton sun kamu da cutar Ebola a wasu kasashe daban, a halin yanzu, tana kokarta wajen gudanar da bincike kan lamarin.
Hukumar WHO ta kuma kara da cewa, cutar ba ta yaduwa ta hanyar iska, dalilin da ya sa, akwai wuya ma'aikatan dake aiki a kamfanonin sufuri musammun ma na jiragen sama su fuskanci barazanar kamuwa da cutar sosai. Hukumar ta yi kira ga wandannan kamfanoni da su tsai da kudurori bisa binciken kimiyya, tare da fatan kuma za su ci gaba da kai kayayyakin agaji da na yau da kullum da jama'ar ke bukata zuwa yammacin kasashen Afirka. (Maryam)