Kasar Sin ta mika kayayyakin tallafi ga kasashen Laberiya da Saliyo, domin tinkarar cutar nan mai hadarin gaske ta Ebola.
Yayin bikin mika kayan ga mahukuntan Laberiya da ya gudana a ranar 12 ga watan nan, wanda aka yi a wani ofishin hukumar kula sufurin ruwa, shugaban kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf, ta bayyana cewa Sin sahihiyar abokiya ce ga kasar ta, wadda ke baiwa kasar taimako a fannonin tattalin arziki, da ilmi, da sha'anin noma, da aikin jiyya, da fannin shari'a da sauransu. Haka kuma a cewar ta Sin na baiwa Laberiya tallafi ciki gaggawa, a duk lokacin da bukatar hakan ta bijiro.
A daya hannun kuma, an gudanar da bikin mika kayayyakin tallafi ga kasar Saliyo, a fadar gwamnatin kasar, inda jakadan Sin dake kasar Zhao Yanbo, da mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar suka sanya hannu kan takardar karbar kayayyaki.
A nasa bangare, shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya ce Sin ta shiga gaban sauran kasashen duniya, wajen baiwa kasar sa tallafin tinkarar cutar Ebola. Don haka ya godewa gwamnatin kasar Sin da jama'arta bisa hakan.
Mr. Koroma ya kara da cewa, Saliyo tana kokarin tinkarar kalubalolin da Ebola ta haifar, za kuma ta yi iyakacin kokarin magance yaduwar wannan cuta cikin makonni masu zuwa, ta hanyar kara zakulo masu dauke da ita, da kafa karin cibiyoyin jiyya, da dai sauran matakai daban daban, ta yadda za a kawar da illar gurgunta tattalin arziki da al'ummar Saliyo ke fuskanta sakamakon yaduwar cutar ta Ebola. (Amina)