Nabarro wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya ce kamata ya yi a fidda managartan shirye-shirye a fannonin daban daban, domin fuskantar kalubalen yaduwar wannan cuta.
Ya ce matsalar da ake fama da ita ba ta tsaya ga hukumomin kiwo lafiya kadai ba, domin kuwa ta ba da nasaba da batun zamantakewar al'umma, da tattalin arziki, da kuma harkokin siyasa. Batutuwan da muddin ba a warware su ba, mai iyuwa ne za a fuskanci babban kalubale ga ayyukan jin kai, da na siyasa da tsaro. Don haka ne Mr. Nabarro ya bayyana bukatar nuna goyon baya kan dukkanin harkokin da suka shafi wannan cuta daga dukkanin fannoni.
Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya nada Mr. Nabarro a matsayin babban jami'i mai kula da harkokin cutar Ebola na MDD ne a ran 12 ga watan da muke ciki. Da ma kuma Mr. Nabarro babban masani ne a fannin harkokin kiwon lafiya, na hukumar lafiya ta duniya WHO. (Maryam)