Jami'an hukumar lafiya ta kasar Sin sun jaddada a Juma'a cewar, a hana a gudanar da gwaje-gwajen kwayar cutar Ebola a cikin fadin kasar, har sai wadanda suke muradin gudanar da irin wannan gwajin sun samu izinin gwamnati.
Hukumar kula da lafiya da tsarin iyali ta kasar Sin, ta ce, gudanar da gwaji a kan kwayoyin cutar virus da gudanar da aune-aunen cutukan dabbobi, dole ne a gudanar da su a ofishin bincike wanda aka sanyawa magungunan kariya na kwayoyin cutuka.
Hukumar lafiyar ta kasar Sin ta dauki wannan mataki ne domin kara tsaurara matakai sakamakon bullar cutar Ebola, wacce ta kashe mutane fiye da dubu daya a Afrika ta yamma.
Hakazalika hukumar ta ba da umurni cewa, dole ne a tsabtace sharar da aka yi gwajin cutar Ebola, kamin a bisne sharar ta hanyar sa mata magani, kuma hukumar ta bukaci da a yi amfani da sharuddan kariya da suka dace a yayin da ake jigila ko gudanar da gwaje-gwaje a kan cutar Ebola mai saurin kisa. (Suwaiba)