in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar kwararru masana a kan cutar Ebola daga kasar Sin sun isa Guinea
2014-08-19 10:57:00 cri

Tawaga ta biyu wacce ta kunshi kwararru masana a kan cutar Ebola daga kasar Sin sun isa birnin Conakry dake kasar Guinea a karkashin wani shiri na musamman da gwamnatin kasar Sin domin taimakawa kasashen Africa tunkarar yaki da barkewar cutar Ebola.

Tawagar ta kasar Sin daga birnin Beijing ta kunshi kwararru guda ukku a fannin kiwon lafiyar jama'a a cikin gaggawa. Kuma a cikin tawagar akwai wasu mambobi guda 10, a karkashin ayyukan kasar Sin na kiwon lafiya na musamman karo 24, wadanda za su yi aiki a wani asibitin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Guinea har tsawon shekaru 2.

Wannan tawaga ta biyu daga kasar Sin za ta canji tawagar farko ta kasar Sin, wadda da ma ta dade kasar Guinea, amma a yanzu za ta komo gida kasar Sin, saboda ta kammala ayyukan da aka umurce ta yi na taimakawa 'yan kasar ta Guinea, kuma ta gudanar da aiki kafada- da kafada da tawagar kwararru daga kasar Guinea a inda suka yi musayar kwarewarsu a fannin murkushe cuta da hana yaduwarta.

Haka zalika tawagar farko daga kasar Sin, ta horar da ma'aikatan lafiya na kasar Guinea a kan yadda za su kare kansu daga cutar ta Ebola da kuma magungunan da za a yi amfani da su da dai sauransu. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China