A ranar Laraba ne masu bincike daga kasashen Amurka da Canada suka bayyana cewa, sun samu nasarar amfani da wani maganin gwaji wajen ceto rayukan birai bayan da aka sanya musu kwayar cutar Marburg mai kisa wadda ta yi kama da kwayar cutar Ebola da ta halaka sama da mutane 1,200 a yammacin Afirka a wannan shekara.
A sabon nazarin da aka yi, masu bincike daga jami'ar Texas da kuma kamfanin harhada magunguna da ke da zama a kasar Canada sun sanya wa gwaggon birrai 16 a Angola, kwayar cutar ta Marburg har zuwa lokacin da cutar ta bulla a jikinsu bayan kwanaki uku.
Masu binciken suka ce, dukkan birran da aka ba su maganin na siRNA sun rayu, yayin da sauran wadanda aka kebe suka mutu bayan kwanaki 7 zuwa 9 da saka musu kwayar cutar.
Masana na ganin cewa, sabon maganin zai iya magance cutar Ebola a jikin birrai, idan aka saka musu maganin cikin sa'o'i 48 bayan da suka harbu da kwayar cutar. (Ibrahim)