An yarda a samar da ruwan gwada cutar Ebola da Sin ta fitar
A yau Laraba 20 ga wata, wakilinmu ya samo labari daga kwalejin kimiyya da likitanci na sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin cewa, bisa jerin gwaje gwaje na DNA, wata cibiyar nazari ta kwalejin ta yi nazari da kuma fitar da wani irin ruwan gwada cutar Ebola. Masanan hukumar kiwon lafiya ta babbar hukumar ba da guzuri ta sojan 'yantar da jama'a sun yi nazari akan wannan ruwa, tare da amincewa da samar da shi a hukunce. An bada labarin cewa, kamfanin Puruikang dake birnin Shenzhen zai dauki nauyin samar da ruwan gwada cutar Ebola, domin ba da gudummawa a fannin fasaha kan tabbatar da kamuwa da cutar Ebola cikin sauri da shawon kan cutar a Sin yadda ya kamata.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku