in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kayayyakin tallafin da Sin ta samar sun isa kasashen Afrika uku dake fama da Ebola
2014-08-13 11:05:04 cri

Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Sun Jiwen, ya bayyana isar kayayyakin kula da lafiya, da gwamnatin kasar Sin ta samar ga kasashen yammacin Afrika uku da ke fama da cutar nan ta Ebola.

Mr. Sun ya ce wadannan kayayyakin da kudin su suka kai RMB miliyan 30, sun isa birnin Konakry hedkwatar Guinea, da birnin Freetown hedkwatar Saliyo da kuma Monrovia hedkwatar kasar Laberiya, tsakanin ranekun 11 zuwa 12 ga watan nan.

Wannan ne dai karo na biyu da Sin ta baiwa kasashen Afrika da ke fama da cutar Ebola tallafi na kayayyakin kula da lafiya. A cewar Mr Sun, masanan kiwon lafiya 9 da Sin ta tura zuwa wadannan kasashen Afrika sun isa wuraren aikin su a ranar 11 ga wata.

Kaza lika mahukuntan wadannan kasashe sun nuna matukar godiya ga tallafin da Sin take ba su, baya ga yabo da hukumomin kasa da kasa ciki hadda kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO suka yiwa wannan kwazo na kasar Sin.

Dadin dadawa, Mr Sun ya ce, ofisoshin jakadancin kasar Sin dake wadannan kasashen uku, da masanan kiwon lafiya na kasar Sin za su taimakawa gwamnatocin wadannan kasashe wajen horas da ma'aikata hanyoyin amfani da kayayyakin tallafi cikin lokaci yadda ya kamata.
Gwamnatin kasar Sin dai na kallon cutar Ebola a matsayin annoba dake addabar yammacin Afrika, tare da jefa sauran kasashen duniya cikin barzana. Don haka Sin ke kira ga kasashen duniya da su dauki matakan da suka dace, domin baiwa kasashen dake fama da yaduwar wannan cuta taimako, ta yadda za su samu nasarar tinkarar mawuyacin halin da suke ciki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China