Jirgin sama kirar Boeing 747 ya isa tun ranar Litinin a Conakry babban birnin kasar Guinea shake da ton 80 na kayayyakin likitanci da kasar ta bada taimako zuwa ga kasashen uku da suka fi fama da cutar Ebola wato Guinea, Liberiya da Saliyo.
A filin saukar jiragen sama na Conakry, jakadan kasar Sin Bian Jianqiang ya mika wa ministan harkokin wajen kasar Guinea, mista Koutoubou Sanoh ton 24 na kayayyakin likita, magunguna da magungunan wanke da kashe cuta da darajarsu ta kai Yuan miliyan 10 wanda ya yi kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.6. (Maman Ada)