Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas, ya bayyana amincewar al'ummarsa, da shirin tsagaita bude wuta da kasar Isra'ila, karkashin shirin da Masar ta jagoranta, ko da yake kungiyar mayakan Hamas ta nuna rashin gamsuwa da hakan.
Bayan bayyana kudurin tsagaita wutar, na daren jiyan Asabar kuma, shugaba na Palasdinu ya jagoranci taron kolin kungiyar Fatah a birnin Ramallah can a yammacin gabar kogin Jordan. Inda yayin taron shugaba Abbas ya bayyana cewa, Masar ta wuce matsayi mai shiga tsakani, domin a cewarsa ita abokiya ce da zai yi wuya a iya maye gurbinta.
Ya ce a nata bangare, Palasdinu na fatan tabbatar aiwatar da shirin dakatar da bude wuta a zirin Gaza ba kuma tare da wani bata lokaci ba, hakan ne kuma ya sanya ta amincewa da shirin da Masar ta gabatar.
Game da batun kin amincewar Hamas da shawarar tsagaita wutar kuwa, daya daga kusoshinta Ezzat al-Resheq, ya ce kamata ya yi shirin da aka gabatar ya biya dukkan bukatun Palasdinu. A daya hannun kuma babban jami'in Hamas a zirin Gaza Ismail Radwan, ya ce Hamas ba ta yarda da dakatar da tattaunawa kan batun filin saukar jirgin sama da tashar jiragen ruwan dake zirin na Gaza ba. (Amina)