Wadannan kalamai sun fito daga bakin Ziad Nakhleh, wani shugaban kungiyar Jihad Islamic dake halarta a yanzu haka a shawarwarin dake gudana a birnin Alkahira a karkashin jagorancin kasar Masar domin cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Palesdinu da Isra'ila.
Wata babbar tawagar Falesdinu ta hada da wakilan kungiyar Hamas, Jihad Islamic da kuma hukumar OLP na tattaunawa a yanzu haka tare masu shiga tsakani na kasar Masar kan wata yarjejeniyar tsagaita wuta tare da Isra'ila da za ta taimakawa wajen kawo karshen rikici na fiye da makonni hudu.
Cikin wannan lokaci kuma, Mouchir al-Masri, wani babban jami'in kungiyar Hamas ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an samu babban ci-gaba a shawarwarin Alkahira.
Ministan kiwon lafiya na Palesdinu a Gaza ya fitar da wata sanarwa cewa, adadin yawan mutanen da aka kashe ya cimma 1868 yayin da mutane fiye da 9470 suka jikkata tun farkon harin Isra'ila kan zirin Gaza a ranar 8 ga watan Juli.
A bangaren Isra'ila a kalla soja 64 tare da fararen hula uku suka mutu, a cewar kafofin watsa labaran Isra'ila. (Maman Ada)