Kakakin sojojin Isra'ila Laftana kanar Peter Lerner wanda ya tabbatar da hakan yayin taron manema labarai, ya kuma ce za su ci gaba da kai hare-hare ta kasa kan yankin na Gaza.
Ya ce, Hamas ta harba rokoki kimanin 8 zuwa Isra'ila, bayan da yarjejeniyar ta fara aiki, koda yake babu wanda ya jikkata. An kuma bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun mayar da martani da makaman atilare kan yankin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, lamarin da a cewar ma'aikatar lafiya ta hukumar Palasdinu ya yi sanadiyar rayukan a kalla Palasdinawa 27.
A yau ne dai yarjejeniyar ta fara aiki, amma ta rushe nan da nan lokacin da Isra'ila ta kai harin da ya halaka Palasdinawa 27.(Ibrahim)